Tawagar Yan Jarida ta ziyarci KH Dass, Tafawa Balewa da Bogoro don duba ayyukan Gwamnatin Bala Mohammed.

Daga Ibrahim Jungudo.

 

Tawagan ‘Yan Jarida a jahar Bauchi, karkashin jagorancin Komishinan Yaɗa Labarai da Sadarwa Alhaji Usman Shehu Usman ta ziyarci Ƙananan Hukumomin Bogoro Tafawa Balewa da kuma Dass a cigaba da duba ayyukan da Gwamnatin Sanata Bala Abdulkadir Mohammed tayi.

A Ƙaramar Hukumar Bogoro, tawagan ta duba hanyar da akeyi a Gambar mai tsawon kilomita 29.

Daga nan sai tawagan ta ziyarci ginin da akeyi a fadar Hakimin Bogoro da kuma Sakatariya Ƙungiyar kiristoci wato CAN reshen Ƙaramar Hukumar.

A Tafawa Balewa kuma, tawagar taziyarci wasu daga cikin ayyukan da akayi kamar hanyoyi da kuma fadar Hakimai da Dagatai a yankin.

Yayinda tawagar ta isa garin Dass, Shugaban Ƙaramar Hukumar Comrade Muhammad Abubakar Jibo, ya zaga da Yan jaridun wasu muhimman ayyukan kamar fadan Mai Martaba Sarkin Dass Alhaji Usman Bilyamu Othman, hadi da gidajen Hakimai da Dagatai a yankin.

Leave a Reply